Za a rage farashin fetur a Nigeria

Image caption 'Yan bumburutu na cin kasuwa

Ministan man fetur na Najeria, Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta yanke hukuncin rage farashin man fetur daga Naira 87 zuwa 85 a kowace litar man.

Ministan wanda ya bayyana haka, yayin wata tattaunawa da ya yi da 'yan jarida a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, ya ce ragin zai fara ne daga ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekara.

A cewar Ministan, gwamnati ta dauki wannan matakin ne bayan da ta yi nazarin hawa da saukar da farashin mai ke yi a kasuwar duniya.

A bayan dai gwamnatin Najeriya ta sha alwashin cewa za ta dinga yanke farashin mai gwargwadon yadda yake a kasuwar duniya.

Haka kuma ta dauki matakin rage fashin ne don tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu yaudara a cikin batun.