Haske zai lullube duhu — Sarauniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarauniya Elizabeth na son ganin lokacin da za ta kai shekaru 90

Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta yi amfani da jawabinta na bikin Kirismeti wajen bayyana cewa haske zai lullube duhu a shekara mai zuwa.

Jawabin na zuwa ne a wannan shekarar da aka fuskanci hare-haren ta'addanci a duniya, ciki har da wanda aka kai a Paris da kuma na wajen shakatawa a Tunisia.

Sarauniyar ta kuma bayyana cewar ta zaku ta ga shekara mai zuwa a yayin da za ta cika shekaru 90 a duniya.

A fadar Vatican, Fafaroma Francis ya jagorancin wata addu'ar Mass a jajiberen Kirsimetin, inda ya yi kira ga Kiristoci da su mutunta rayuwa.