Kiir ya kirkiro jihohi a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kiir na takun saka da Machar

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya fitar da wata dokar kirkiro da sabbin jihohi 28 daga cikin goman da ake da su.

Masu sharhi sun ce wannan mataki na ba-zata, ka iya yin zakon kasa ga yarjejeniyar raba madafun iko da aka cimma a cikin watan Agusta, domin kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru biyu ana fafatawa a kasar.

A ranar Litinin ne, 'yan tawaye kimanin dari da hamsin suka dawo Juba, babban birni kasar domin fara gudanar da aiki kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Sun kuma ce yanzu haka suna yin nazari kan illolin dake tattare da wanan doka ta ba zata, da aka fitar yammacin ranar Alhamis.

A makon jiye ne, wata kungiya mai sa ido kan tashe-tashen hankula ta kasa da kasa ta yi gargadi kan yarjejenuiyar zaman lafiyar, Sudan ta Kudun da cewa akwai kungiyoyin masu rike da makamai da dama da basa goyon bayan ko wane bangare.