An kashe babban kwamanda 'yan tawaye a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana shirin kawo karshen zubar da jini a Syria

An hallaka babban kwamandan daya daga cikin kungiyoyin 'yan tawaye mafi girma a Syria, sakamakon hare-haren da jiragen yakin Rasha suka kai.

'Yan tawaye sun ce jiragen yakin Rasha sun kashe Zahran Aloush, shugaban kungiyar Jaysh al-Islam a lokacin da aka kai hari a shalkwatar kungiyar da ke kusa da Damascus.

Rahotanni sun ce an kashe har da wasu jiga-jigan kungiyar a lokacin harin.

Wakilin BBC a gabas ta tsakiya, ya ce kashe Mr Aloush babban sako ne, a yayin da ake kokarin sulhu tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Syria wacce ke samun goyon bayan Rasha.