Za a soma kwashe 'yan tawaye daga Yarmouk

Hakkin mallakar hoto Amaq
Image caption Za a kwashe hadda 'yan kungiyar IS

Rahotanni na cewa motocin safa sun isa sansanin 'yan gudun hijira na Yarmouk a kasar Syria, gabanin kwashe mayaka 'yan tawaye da suka hada da 'yan kungiyar mayakan IS da iyalansu da ake sa ran gudanarwa.

Babu tabbaci kan lokutan yarjejeniyar wacce Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani, amma kuma gidan talabijin na Hezbollah ta ce motocin safa-safa 18 na nan a kasa, da za su kwashe 'yan tawayen daga sansanonin da aka yi wa kawanya a kudancin birnin Damascus.

Za a bai wa dukkaninsu hanyoyin ficewa cikin kwanciyar hankali zuwa birnin Raqqa inda suka fi rinjaye.

Hakan kuma zai baiwa Majalisar Dinkin Duniya damar kai kayyakin agajin da ake bukata a Yarmouk din, da galibi Falasdinawa 'yan gudun hijira suka fi yawa.