Ingila: Bala`in Ambaliyar ya Afka wa Jama`a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ambaliyar ruwa a Ingila

Wani mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwan da ta tilasta wa jama'a fita daga daruruwan gidajensu a arewacin Ingila.

Kazalika kusan gidaje dubu goma ne ke fama da rashin wutar lantarki, yayin da aka yi ta kwashe tsofaffi da sauran mutane masu rauni da kwale-kwale.

Wakilin BBC ya ce ana amfani da manyan injunan wuta ko Janareta wajen haska wurare don taimaka wa sojoji ta yadda za su kashe dare suna aiki, inda suke girke buhunan yashi da injunan zuke ruwa.

A halin da ake ciki sama da gidaje dubu uku da ke bakin kogi a arewacin birnin York na fuskantar hadari, sakamakon tumbatsar da koguna ke yi.

A gobe Litinin ne ake sa-ran Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron zai ziyarci wuraren da bala'in ya shafa.