Sojojin Iraqi suna dannawa cikin Ramadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Iraqi a Ramadi

Sojojin Iraqi tare da taimakon farmaki ta sama da Amirka ke jagoranta sun kusa kaiwa wasu rukunin gine ginen gwamnati a birnin Ramadi a mummunan barin wuta da suke yi da mayakan kungiyar IS. Wani mai magana da yawun sojin Iraqi Brigadier Yahya Rasool yace bai fi tazarar kilomita daya ba tsakanin su da rukunin gine ginen. Yace babban abin da suka maida hankali a kai shine kaucewa hasarar rayukan fararen hula. Fafatawar ta baya bayan nan na zuwa ne yayinda sojojin Iraqin ke cigaba da kara matsa kaimi domin sake kwace birnin na Ramadi wanda ya fada hannun yan tawayen IS a cikin watan Mayu.