Niger: Mahaman Ousman zai tsaya takara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mahaman Ousman

A Jamhuriyar Nijar Jam'iyyar MNRD Hakuri ta tsaida Alhaji Mahaman Ousman a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa na 2016.

Wannan dai shi ne karo na farko a cikin tarihin siyasar kasar da wata jam'iyya ta tsaida wani da ba dan jam'iyar ba ya mata takara.

A baya dai Mahaman Ousman ya kasance jagoran jam'iyyar CDS Rahama kafin rikicin siyasa ya dara jam'iyyar, shugabancinta kuma ya koma hannun Abdou Labo.

Hakan ne ya sanya jama'a suka zura ido domin ganin ko a wace jam'iyar Mahaman Ousman zai tsaya takarar shugabancin Nijar a 2016.

Jam'iyyar MNRD Hakuri dai ta ce ba bu kuskure a matakin da ta dauka, yayin da magoya bayan Mahaman Ousman ke alasan barka game da lamarin.