Boko Haram: An kashe mutane 14 a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption boko haram

Rahotanni daban-daban dai sun ruwaito cewa a garin Kimba da ke cikin jihar Borno da ke yankin arewa masu gabashin Najeriya ,wasu da ake zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wani hari a ranar juma'ar da ta gabata.

A cikin wannan harin cewar rahotannin yan kungiyar sun kashe akalla mutane 14 tare da jikita wasu da dama a wani yanayin budai wuta irin na kan mai tsautsayi, tare da kona wani bangare na gari kafin su fice daga kauyen.

Kuma maharan sun yi amfani da Kekuna ne wajen kai harin.

Yan kungiyar dai sun shiga garin na Kimba da musalin karfe goma na dare kamar yadda wanni dan kwato da gora da ya shaida lamarin ya tabbatar.

Wannan lamari na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a cikin wata hira da BBC ya sanar da cewa sojojin Najeriya sun karya lagon yan kungiyar ta Boko Haram.