Shirin tattaunawar sulhun kan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Steffan de Mistura yace yana fatan taron tattaunawar sulhun wanda za a gudanar a birnin Geneva zai sami halartar wakilan gwamnatin shugaba Bashar al Assad da kuma na yan adawa

Wani mai magana da yawun jakadan musamman din na Majalisar Dinkin Duniya yace ba za a bari halin da ake ciki a kasar ta Syria ya kawo nakasu ga tattaunawar ba.

Yace Mr de Mistura na fatan samun hadin kai daga dukkan bangarorin.