Sojoji sun dakile hari a Maiduguri

Image caption Sojin Nigeria sun sha alwashin murkushe Boko Haram zuwa karshen shekara

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke yaki da kungiyar boko haram a shiyyar arewa maso-gabashin kasar sun dakile yunkurin wasu 'yan kunar-bakin-wake su goma da suka yi niyyar kai hari birnin Maiduguri ta hanyar murkushe su, ranar Lahadi da maraice.

Rundunar ta ce dakarunta sun yi nasarar dakile harin ne bayan sun kama wasu 'yan kunar-bakin-wake biyu, wadanda suka fallasa aniyar mayakan Boko Haram din ta kai hari birnin na Maiduguri.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Gangamin da ake yi wa taken Lafiya Dole, wato Kanar Mustapha Anka ya fitar, rundunar sojin Najeriyar ta ce dakarunta sun yi wa 'yan boko-haram din kwanton-bauna ne a kan hayar Damboa da Babbar Kotun jiha da kuma Asibitin Ido, inda suka murkushe su.

Rundunar sojin na maida martani ne ga rahotanni da ke cewa mayakan Boko Haram sun kai hari kusa da birnin Maiduguri, labarin da rundunar ta ce ba gaskiya ba ne.

Sai dai a bangare guda, wasu da lamarin ya auku a kan idanunsu, sun shaida wa BBC cewa hari ne wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai, a kauyukan Aljawari da kuma unguwar Jiddari Polo a kusa da birnin Maidugurin, kuma har wata roka ta yi sanadin mutuwar mutane uku.

Amma ba a fayyace ba ko roka daga bangaren sojojin Najeriya ne ko kuma mayakan boko haram ba.