An bizne daya daga cikin maharan Paris

Dan sanda na taimaka wa wanda hari a shafa a Bataclan Hakkin mallakar hoto Reuters

Jami'ai a Paris sun ce an bizne daya daga cikin mutanen da suka kai mummunan harin nan a babban birnin Faransan cikin watan da ya wuce, a wani kabarin boye.

Sun ce an rufe Samy Aminour ne ranar alhamis a wata unguwar bayan birnin Paris ta Seine Saint Denis a inda mahaifansa keda zama.

Yana daya daga cikin yan kunar bakin wake 3 da suka halaka mutane casa'in da suka je wajen wani taron kide - kide da rawa a Gidan rawa na Bataclan.

Ana jin shi ne na farko daga cikin maharan da aka bizne.

Mutane 130 ne dai suka mutu a hare haren a ko'ina cikin Paris a ranar 13 ga watan Nuwamba