Rouhani ya soki kasashen Musulmi

 Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Kasar Iran

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya bukaci kasashen musulmi da su tinkari tashin hankalin da ya ce yana baiwa addinin musulunci mummunan suna.

Da yake jawabi ga wani taro a Tehran, Shugaba Rouhani yayi magana kan abun kunyar tilasta wa musulmai yin mawuyatan tafiye tafiyen domin neman mafaka a kasashen da ba na musulmi ba.

A wani shagube ga Saudiya da kawayenta na yankin Gulf, ya soki kasashen da ya ce na sayen makaman Amurka sannan su yi amfani da su kan yan uwansu musulmi.