Nigeria za ta dauki 'yan civilian JTF aikin soja

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Civilian JTF na taimaka wa sojoji a yaki da Boko Haram

Gwamnatin Nigeria ta ce za ta soma daukar matasan nan masu taimaka wa sojan kasar wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ka fi sani da civilian JTF, aikin soja.

Ministan tsaron kasar Birgadiya Janar, Mansur Dan Ali mai ritaya ne, ya sanar da hakan bayan wani rangadin da ya yi a jihohin da suka fi fama da hare-haren kungiyar ta Boko Haram.

Dan Ali ya ce "Yara ne matasa wadansu daga cikinsu na ba mu labarai masu muhimmanci, shi ya sa muka ga ya dace mu dauki wadansu daga cikinsu saboda suna da kwarewa ta shiga aikin soja."

Ministan ya ce za su tantance kafin su dauki matasan a aikin soja, saboda gudun kada 'yan Boko Haram sun yi shigar burtu su saje, cikin wadanda za a dauka a aiki.

Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane fiye da 17,000 sannan wasu fiye da miliyan biyu sun rasa muhallansu.