An kafa tutocin Iraki a Ramadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Lahadi aka kwace Ramadi daga hannun 'yan IS

Sojojin Iraki sun kafa tutar kasar a farfajiyar ginin da ke dauke da ma'aikatun gwamnati da ke tsakiyar birnin Ramadi, bayan sun fatattaki mayakan kungiyar IS a ranar Lahadi.

Kwace ginin daga ikon kungiyar IS, shi ne abin da sojojin suka dade suna hankoro.

Mai magana da yawun sojojin Iraki , Birgediya Janar, Yahaya Rasool ya ce sunkwato birnin Ramadi.

Kuma jami'an tsaro masu yaki da ta'addanci sun kafa tutar kasar a gine-ginen gwamnati da ke Anbar.

A watan Mayu ne dai kungiyar IS ta kama birnin bayan da ta yi wa sojojin gwamnatin korar kare.