An soma kwashe fararen hula a Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwashe fararen hula na karkashin yarjejeniyar zaman lafiya

Ana kwashe mayaka da fararen hula daga wani yanki na Syria da ke hannun 'yan tawaye, wanda sojin gwamnati suka dauki tsawon lokaci suna yi masa kawanya.

Motocin safa-safa da ke dauke da kamar mutane dari sun bar garin Zabadani da ke yammacin kasar.

A karkashin wata yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi jagorancin samarwa, an bari a fitar da wadanda aka kwashe din cikin amince.

Da farko za su nufi Lebanon ne, kana su nufi Turkiya.

Tarikh Wahabi na kundiyar agaji ta ICRC ya ce aikin kwashe mutanen ana yinsa ne bisa hadin gwiwar ICRC da ke Lebanon da Syria da kuma kungiyar agajin gaggawa ta Lebanon tare da kungiyar agaji ta Syria da kuma majalisar dinkin duniya.