Al-Abadi ya ziyarci Ramadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Iraki na murnar kwace iko da Ramadi

Firai ministan Iraki, Haider al Abadi ya ziyarci birnin Ramadi, kwana guda bayan da dakarun gwamnatin kasar suka kwace iko da birnin daga hannun 'yan kungiyar IS.

Mr Abadi ya isa kudancin birnin a jirgi mai saukar angulu.

Ya jinjina wa dakarun kasar saboda namijin kokarin da suka yi na kakkabe mayakan IS daga manyan tintunan birnin.

Sai dai wasu rahotanni sun ce, ana jin karar harbe-harbe a wasu sassa na birnin, inda bayanai suka ce dan kunar bakin wake ya hallaka sojoji da dama a wani lardi da ke arewacin Ramadi.

Tuni sakataren tsaron Amurka, Ash Carter ya jinjina wa sojojin Irakin dangane da kwato birnin Ramadi, yana cewa wani muhimmin yunkuri ne na maurkushe kungiyar IS.

Mr Carter ya ce, ya kamata Iraki ta tsaya, tsayin-daka wajen wanzar da zaman lafiya a Ramadi tare da tabbatar da cewa birnin bai koma hannun mayakan IS ba.