Kabore ya sha rantsuwar kama aiki

Hakkin mallakar hoto

Sabon shugaban kasar Burkina Faso, Mark Christian Kabore, ya sha rantsuwar kama aiki, bayan nasarar lashe zaben shugabancin kasar.

Mista Kabore wanda tsohon firai ministan kasar ne, ya kasance aboki ga hambararren shugaban kasar na Burkina Faso, Blaise Compaore, wanda ya kwashe shekaru 27 a kan karaga bayan da ya yi juyin mulki.

Kabore ya raba gari da mista Compaore ne bayan da Compaoren ya ayyana aniyarsa ta ci gaba da mulkin kasar.

Kimanin shugabannin kasashe biyar ne a nahiyar Afirka ke halartar bikin ransuwar.