WHO: Ebola ta bar kasar Guinea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption guinea

'Yan kasar Guinea dai sun gudanar da shagulgulan kawo karshen wannan cuta mai halaka jama'a tare da yin kade-kade da raye-raye.

Da dama daga ciki su na ganin cewa wannan wani farko ne na aza sabon tubali ga kasar, a daidai lokacin da ake fuskantar shiga sabuwar shekara da kuma soma waadi na biyu kan kujerar mulkin shugaban kasar Alpha Conde .

To sai dai duk yadda lamarin ya kasance,da akwai wuya 'yan kasar ta Guinea su manta da mutane 2083 maza da mata da suka mutu sanadiyar kamuwa da cutar Ebola, da kuma irin tasirin da cutar ta yi kan rayuwar al'ummar kasar da ma tattalin arzikin ta.

A cewar asusun tallafi ga yara na majalasar dinkin duniya wato UNICEF a kasar ta Guinea, yara 6220 ne su ka kasance marayu ,ko dai sun rasa daya kuma duka biyu daga cikin mahaifansu sanadiyar Ebolar.

Wadanda suka tsira da cutar na rayuwa cikin fargaba da tsoro da kuma zulumi na dogon lokaci game da cutar.

Wani malamin jami'a da na sadu da shi a watan Janairu a Conakry, a gaggauce ya dora laifi game da wannan lamari na Ebola a kasar ta Guinea kan kasashen yammacin duniya da gwamantin kasar.