Bam ya hallaka mutane 22 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumomi a Pakistan sun kai mutanen da suka jikkata zuwa asibiti

'Yan sanda a arewa maso yammacin Pakistan, sun ce akalla mutane 22 ne suka rasu sannan da dama suka jikkata a wani harin kunar-bakin-wake a garin Mardan.

Dan kunar-bakin waken dai wanda yake a kan babur, ya daki kofar shiga wani ginin gwamnati a inda mutane suke a kan layukan karbar katin dan kasa suka rasu.

Wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru, ya ce wurin da abin ya faru ya yi kaca-kaca da sassan jikin mutane da gilasai.

Wannan dai shi ne harin da yafi kowanne muni a shekarar 2015 bayan an samu tsaikon hare-hare.

Wani bangare na kungiyar Taliban mai suna, Jama'atul Ahrar ya dauki alhakin kai harin.