Akalla mutane 22 ne suka rasa ransu a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sanda a arewa maso yammacin Pakistan sun ce akalla mutane 22 ne suka rasa ransu sannan da dama suka jikkata a wani harin kunar-bakin-wake a garin Mardan.

Dan kunar-bakin waken dai wanda yake a kan babur ya daki kofar shiga wani ginin gwamnati a inda mutane suke a kan layukan karbar katin dan kasa.

Wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru ya ce wurin da abin ya faru ya yi kaca-kaca da sassan jikin mutane da buraguzan gilasai

Mai magana da yawun wani bangare na kungiyar Taliban, mai suna, Jama'atul Ahrar a wani sako ta kafar imel ta dauki alhakin kai harin, ta kuma ce duk wasu gine-ginen gwamnati sun halatta su kai musu hari.