Buhari zai gana da 'yan jarida

Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin yin yaki da karbar hanci da rashawa.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai yi ganawarsa ta farko da 'yan jaridar kasar a fadarsa da ke Abuja.

Ganawar -- wacce za a watsa kai-tsaye ta kafafen yada labaran kasar -- za ta mayar da hankali ne kan babutuwa da dama, kuma za a yi ta ne da misalin karfe bakwai na yamma a agogon Najeriya.

Shugaban kasar zai gana da 'yan jaridar ne a daidai lokacin da matsaloli ke kara yin yawa a kasar, kuma ake zargin ba ya yin hira da kafofin watsa labaran cikin gida.

Hare-haren kunar-bakin-waken da ake ci gaba da kai wa a arewa maso gabashin kasar tun bayan da Shugaba Buhari ya karbi mulki a watan Mayu sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Kazalika, darajar kudin kasar, Naira, na ci gaba da faduwa a daidai lokacin da ake fama da karancin man fetur.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta fara kama mutanen da ake zargi da sace kudaden kasar da karbar hanci da rashawa, musamman mutanen da aka dorawa alhakin sayo makamai domin bai wa sojoji su yaki kungiyar Boko Haram.