Nkurunziza ya yi wa dakarun AU barazana

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Nkurunziza na fuskantar matsin lamba

Shugaban kasar Burundi, ya yi barazanar yakar duk wata rundunar da kungiyar Tarayyar Afirka za ta tura idan ta sa kafa a kasarsa.

Da yake jawabi a gidan rediyon gwamnatin kasar, Shugaba Pierre Nkurunziza ya ce zai dauki kasancewar dakarun kiyaye zaman lafiyar, a matsayin wani mataki na keta martabar Burundi, da kuma hari a kan gwamnatinsa.

Mista Nkurunziza, wanda ya koma kan kujerarsa a karo na uku a wani yanayi mai cike da kace-na-ce, bai halarci kaddamar da rundunar ba a ranar Litinin.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi gargadin kakaba takunkumi, idan ba a koma kan teburin shawarwari ba a watan Janairu.