Ana zaben shugaban kasa a CAR

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al'ummomin Jamhoriyar Tsakiyar Afrika

A ranar Laraban nan ne al'ummomin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka za su fita domin kada kuri'a a zaben shugaban kasar da aka yi ta jinkirtawa, wanda kuma ake fatan zai dawo da mulkin dimokradiyya da kawo karshen rikice-rikice a kasar.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun sha alwashin hana sake aukuwar tashin hankalin da ya faru a kasar lokacin zaben raba-gardama kan sabon kundin tsarin mulki, makonni uku da suka gabata.

'Yan takara 30 ne ke fafatawa a zaben shugaban kasar.

A lokacin da Fafaroma Francis ya ziyarci kasar a farkon wannan watan, ya yi kira ga kungiyoyin 'yan bindiga na Musulmai da Kiristoci da su rungumi zaman lafiya, sannan su fara shirin sasantawa.