Jam'iyyar APC a Kaduna ta shiga ruɗu

Hakkin mallakar hoto Nasir ElRufai Facebook
Image caption Ana zaman doya da manja tsakanin El-Rufai da Shehu Sani

Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Kaduna, da ke arewacin Nigeria na kara kamari.

A yanzu haka, jam'iyyar ta bayar da sanarwar dakatar da daya daga cikin jiga-jiganta watau dan majalisar dattijai da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani.

Jam'iyyar na zargin Sanata Shehu Sani ne da kasa iya bakin sa da nuna raini ga shugabannin jam'iyya da kuma dora shakku a bisa yaki da cin hanci da karbar rashawa na gwamnatin jam'iyyar APC.

Dan majalisar dattijan dai ya yi watsi da zarge-zargen, ya kuma dora alhakin dakatar da shi a kan rikicin da ke tsakanin sa da gwamnan jihar, Malam Nasiru El Rufai.

A kwanakin baya ne wani bangare na jam'iyyar ya balle inda yake zargin uwar jam'iyyar a jihar da nuna rashin iya aiki da kuma rashin alkibila.

Masu sharhi na kallon, barakar da ta kunno kai a jam'iyyar a matsayin somin tabi na abin da ka iya faruwa idan zabukan shekara 2019 suka karato.