Dakarun Syria na lugude a kudancin kasar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yakin basasa ya daidai ta Syria

Dakarun gwamnatin Syria wadanda Rasha ke tallafawa da hare-hare ta sama, na ci gaba da kaddamar da gagarumin hari a yunkurinsu na kwato wani gari mai muhimmanci a kudancin lardin Deraa.

Rundunar sojojin kasa ta Syria, ta ce dakarunta sun shiga garin Shaikh Maskin daga bangarori da dama.

Sai dai wasu majiyoyin 'yan tawaye, sun ce dakarun na wajen gari yayin da ake ci gaba da dauki ba dadi.

Garin dai na kan wata hanya ce mai muhimmanci da ta tashi daga Damascus zuwa babban birnin lardin wanda shi ma ake kiransa Deraa.

Da dama daga cikin 'yan tawayen da ke yankin dai birbishi ne na asalin 'yan adawar da suka bijire wa Shugaba Assad, a maimakon masu tsattsauran ra'ayi da masu da'awar jihadi da suka yi kaka-gida a wasu wuraren.