Ana bincike kan gobara a Dubai

Hakkin mallakar hoto AP

Masu bincike a Dubai sun dukufa domin gano musabbabin tashin gobara a wani babban Otal lokacin da ake shirin bikin shiga sabuwar shekara.

Gobarar ta lashe gefe daya na otan din Address Downtown mai hawa 63, inda aka kwashe mutanen da ke cikinsa da gaggawa.

Mutane da dama sun samu raunuka sanadiyar gobarar.

Duk da hakan dai, an ci gaba da wasannin tartsatsin wuta kamar yadda aka tsara a ginin Burj Khalifa, ginin da ya fi kowanne tsawo a duniya, kuma yake tazarar 'yan mitoci tsakaninsa da otal din da gobarar ta tashi.

Gwamnatin Dubai ta bayyana cewa wutar ta soma ne daga hawa na 20 a otal din.