Kudin sayen motoci bai kai $45b ba— Majalisa

Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya ta musanta yamadidin da ta ce wasu kafofin yada labarai ke yi, cewa ta na shirin kashe makudan kudade don sayen sabbin motoci 400 ga majalisar.

A wata tattaunawa da ya yi shi ma ta musanman da 'yan jarida, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi zama da shugabannin majalisar dokokin a kan wannan yunkuri da ke zuwa a lokacin da kasar ke kukan rashin kudi.

Sai dai Honorable Abdulrazzak Namdaz, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilan Najeriya, ya ce ba gaskiya ba ne zargin da ake yi cewa majalisar dokokin na shirin kashe dala biliyan 45 wajen sayen sabbin motoci.

Namdaz ya ce har yanzu majalisar ba ta zauna ta amince da ire-iren motocin da za su saya ba, kuma basussuka ne za a karbo a sayi motocin da su.

Ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa an bai wa 'yan majalisar basussukan kudaden sayen motoci, inda ya kara da cewa motocin da majalisar ke shirin saya yanzu, na aikin kwamitocinta ne.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa, wasu ne ke naman hada 'yan majalisar fada da 'yan Najeriya shi yasa ake ta yamadidin majalisar na shirin kashe makudan kudade don sayo motocin.