Matar Netanyahu ta amsa tambayoyin 'yan sanda

Image caption Sara da mai gidanta Benjamin Netanyahu

'Yan sanda a Isra'ila, sun yi wa matar Firai ministan kasar, Benjamin Netanyahu tambayoyi bisa zargin amfani kudin gwamnati wajen gyara gidansu na kashin kansu.

Kafoffin yada labarai a Isra'ila, sun nuna hoton wata mota da ta dauki Sara Netanyahu zuwa caji ofis na 'yan sanda.

Ana sa ran za ta amsa tambayoyi a kan amfani da kudin gwamnati, da ake zargin ta biya wajen sayen sabobbin kujerun gida da kuma na gyaran gidan.

An dade ana zargin yadda iyalan Netanyahu ke kashe kudi da kuma yanayin rayuwarsu musamman yadda Sara Netanyahu ake zarginta da yin almubazzaranci da kudi.