Taraba: Kotu ta kori karar Aisha Alhassan

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Aisha Alhassan na da damar daukaka kara

Kotun daukaka kara ta Najeriya ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na ayyana Aisha Alhassan ta jami'yyar APC, a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar Taraba.

A ranar 7 ga watan Nuwamba ne, kotun sauraron kararrakin zabe ta soke zaben Mr Darius Ishaku na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Taraba, ta kuma ce Aisha Alhassan ce ta yi nasara.

Kotun daukaka karar ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis, inda ta kafa hujja da cewa korafin da jam'iyyar APC ta gabatar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe bai kai a soke zaben Mista Ishaku na jam'iyyar PDP ba, wanda tun farkon shi hukumar zabe ta ayyana a matsayin wanda ya ci zaben.

Dukkan mutane biyar na kwamitin da ya yanke hukuncin wanda mai shari'a Abdul Aboki ya jagoranta, sun yi ittifaki cewa kotun sauraron kararrakin zaben ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Aisha Alhassan ke da nasara.

Alkalan sun ce kundin tsarin mulki, ya nuna karara cewa kotun sauraron kararrakin zabe bata da hurumin cewa dan takara bai cancanta ba, sai in har kotu ta taba samun dan takara da wani laifi ko yana taba aikata wani mugun laifi ko kuma in yana cikin wani halin tsananin rashin lafiya.

Rahotanni na cewa 'yar takarar jam'iyyar APC din na da damar daukaka kara zuwa kotun koli.