Ana yin bikin sabuwar shekara cikin tsaro a Turai

Image caption Bikin shigar sabuwar shekara a birnin Paris na faransa

Yawancin biranen kasashen Turai dai na cikin shirin ko-ta-kwana saboda tsoron kai harin ta'addanci a yayin da a ke gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara.

A Jamus, an kwashe mutane daga wasu tasoshin jiragen kasa biyu, an kuma gargadi mutane da su guji taron jama'a bayan da 'yan sanda a Munich suka samu wani bayani game da harin ta'addanci da ake shirin kai wa a birnin.

A Paris, babban birnin Faransa, an soke wasan wutar da ake yi duk shekara yayin da aka karfafa matakan tsaro a kasar.

Cicirindon jama'a ne suka kalli wani hoton bidiyo na minti biyar wanda aka kare shi da haska wasu fitilu masu launuka a kan kofar Arc de Triomphe da ke tsakiyar birnin.

Wannan shi ne taron jama'a mafi girma a birnin tun bayan harin da masu da'awar musulunci suka kai a watan Nuwamban shekarar da ta wuce.

A Rasha, an jinkirta wasan wuta na bikin shiga sabuwar shekarar a Moscow babban birnin kasar na minti biyar.

Sannan a karon farko a tarihi 'yan sanda sun rufe dandalin Red Square inda jama'a suka saba zuwa domin gudanar da taruka.

A Brussels babban birnin Belgium, bukukuwan shiga sabuwar shekarar aka soke dungurungum.

A birnin Landan, an kara yawan 'yan sanda 3,000 a kwaryar birnin, tare da karin wasu jami'an tsaro dauke da makamai.

A Ankara babban birnin Turkiya 'yan sanda sun kama wasu mutane biyu da a ke zargin 'yan kungiyar IS ne, an kama mutanen a bisa zargin kitsa kai hare-hare kan taron jama'a a wurare daban-daban a birnin a yayin bikin shiga sabuwar shekarar.

Rahotannin na cewa an kama mutanen da wasu abubuwa masu fashewa da kuma rigar bama-bama a yayin da 'yan sanda suka kai wani sumame.