Blackberry ya fasa ficewa daga Pakistan

Hakkin mallakar hoto Blackberry

Kamfanin Blackberry ya ce ya shawo kan takaddamar da yake yi da gwamnatin Pakistan a kan sakonnin da jama'a za su rika aika wa, a saboda haka ya ce ya fasa fice wa daga kasar.

A watan Nuwamba ne kamfanin na Blackberry ya sanar da cewa zai fice daga Pakistan, saboda bukatar sa da gwamnatin jihar ta yi na ya ba ta damar sa ido a kan sakonnin da masu amfani da wayoyin Blackberry ke aikawa.

Hukumar da ke kula da sadarwa ta Pakistan din a wancan lokaci, ta ce ta na son sa ido a kan sakonnin ne domin taimaka wa wajen yaki da ta'addanci da aikata laifuka.

Sai dai yanzu, hukumomi a Pakistan din sun janye bukatar ta su.

Wani shugaban kamfanin na Blackberry, Mista Marty Beard ya wallafa a shafinsa cewa, bayan tattaunawa, gwamnatin Pakistan ta yanke shawarar janye kudurin nata, sannan kamfanin ya yarda ya ci gaba da zama a kasar.

Mista Beard ya ce kamfanin ya na godiya ga gwamnatin da kuma hukumar kula da sadarwa ta kasar bisa sauya shawara da suka yi.

Ya ce kamfanin na Blackberry a shirye ya ke ya yi aiki da 'yan sanda a kan wasu zarge zargen aikata laifuka, amma ba zai ba 'yan sanda damar sanin bayanan jama'a ba.