'Za mu gana da Buhari kan 'yan Chibok'

Image caption 'Yan matan Chibok da aka sace a 2014

Kungiyar fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok, watau Bring Back Our Girls ta ce za ta gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan batun ceto 'yan matan.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani taro da ta yi a inda ta ke zama a dandalin Unity Fountain a Abuja.

Kungiyar ta BBG ta nanata rashin jin dadinta da na iyayen yara matan da aka sace da kuma al'ummar garin Chibok mazauna Abuja, kan yadda shugaban Buhari ya ce ba shi da masaniya game da inda 'yan matan su ke, a hirar da yayi da 'yan jarida a ranar Laraba.

A hirar da BBC ta yi da Aishatu Yesufu, daya daga cikin shugabanin kungiyar ta ce,kungiyar za ta gana da shugaban ne a ranar 14 ga wannan watan, domin sanin irin matakin da gwamnati ke dauka na ceto 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan ne su 219 daga makarantar kwana a Chibok a shekara ta 2014.