An kai wa sojojin Indiya hari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sansanin sojin sama na Panthakot na arewacin Delhi babban birnin India

'Yan sanda a Indiya sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani sansanin sojojin sama da ke kusa da kan iyakar Pakistan.

Jami'an gwamnati sun ce an yi amfani da wata motar 'yan sanda da aka sace wajen kai harin a kan sasanin na Pathakot da ke arewacin Delhi, babbban birnin kasar.

Rahotanni na cewa 'ya bindigar su hudu ko biyar sun kai harin ne da misalin karfe 3.30 na agogon kasar, a yammacin ranar Juma'a.

Rahotannin sun kara da cewa an kashe wasu daga cikin 'yan bindigar, sannan kuma an yi wa sauran kawanya.