Ana zaman dar dar a Munich

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'an tsaro sun yi gargadin yiwuwar harin kunar bakin wake daga kungiyar IS a birnin Munich.

Jami'an tsaro a Munich dai sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar kai harin kunar bakin wake a birnin, inda suka tsaurara bincike a tashoshin jiragen kasan da suka koma bakin aiki.

Wata 'yar sanda ta ce bayanin da suka samu na cewar kungiyar IS na shirin kai harin kunar bakin wake, ya fito ne daga hukumar leken asiri ta Faransa.

An rufe tashar jiragen da ke tsakiyar birnin tun a daren jiya, inda 'yan sanda ke neman wasu 'yan Iraki da Syria su kusan bakwai da suke zargi da yunkurin kai harin.

'Yan sanda sun rufe tashoshin jiragen ne sa'o'i kadan kafin sha biyun daren ranar Alhamis, sakamakon abunda suka kira muhimmin bayanin da ke cewa akwai yiwuwar samun harin kunar bakin wake a garin.

Shugaban rundunar 'yan sandan na Munich Cif Hubertus Andrae, ya ce hukumar tana bincikar wasu sunayen da ke cikin tsarin alkaluman ta, ya kuma bukaci mazauna birnin da ke kudancin Jamus din, da su ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba.