Nigeria: 'Ba a hana sanya hijabi ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan makaranta sanye da hijabi

Fadar shugaban Najeriya ta yi watsi da jita-jitar da a ke yadawa cewa gwamnatin kasar ta haramta sanya hijabi, wanda ta ce shi ne alamar kamalar mace musulma.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar bayan wata hira ta musamman da shugaba Buhari ya yi a gidan talabijan na kasar ranar Laraba, mataimakin shugaban na musamman kan harkokin watsa labarai Mallam Garba Shehu, ya ce rade-radin ba shi da makama.

Jami'in ya kara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da daukaka mutunci da hakkin mata musulmai a kasar, sannan kuma ya ce kowa yana da damar bin addinin da ya ke so.

Duk da cewa mataimakin ya bayyana cewa 'yan ta'adda na amfani da hijabi wajen aiwatar da munanan ayyuka kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ya ce gwamnati ba za ta dauki wani tsattsauran mataki ba, ba tare da shawara ba.