BH: Za a gyara garuruwan da aka lalata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a gyara makarantu da gidaje

Shugaban Najeriya ya ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta kaddamar da kwamitin gyara kayayyakin da aka lalata, a garuruwan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kori jama'a, a arewa maso gabashin kasar.

Shugaban ya ce kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Janar Theophilus Danjuma mai ritaya.

Haka kuma hanshakin dan kasuwan nan da ya fi kowa arziki a Afirka, Alhaji Aliko Dangote zai zama mamba a kwamitin.

Kwamitin zai kuma yi aikin sake tsugunar da mutanen da kungiyar ta Boko Haram ta sa su gudun hijira.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ta ce kwamitin zai tafiyar da duk kan tallafin da za a samu daga cikin gida da kasashen waje.

Sanarwar ta ce kayayyakin da kwamitin zai gyara sun hada da hanyoyin mota da makarantu da wuraren ibada da sauransu.