Kungiyar Taliban ce ta kai hari Kabul

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin da aka kai gidan abinci a garin Kabul.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kai wani gidan abinci a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Jami'an kasar sun ce an kashe akalla farar hula hudu sakamakon harin da aka kai wajen gidan abincin Le Jardin, daya daga cikin kananan gidajen abincin da har yanzu bakin kasar ke ziyarta a Kabul, wanda ke shiyyar Taimani.

Wani dan jarida a garin na Kabul, wanda mazaunin kusa da wurin ne ya ce fashewar bam din ta tarwatsa gilasan tagogin gidaje a unguwar.

A 'yan watannin baya-bayan nan dai mayakan Taliban din sun zafafa kai hare-hare ga duk wata matattarar baki daga kasashen waje, inda mutane shida ciki har da jami'an tsaron kasar Spaniya su biyu ke cikin wadanda aka kashe a wani samame da mayakan suka kai wani gida da ke karkashin kulawar ofishin jakadancin Spaniya a watan Disamba.