Al-Shabab ta fitar da sabon bidiyo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al Shabab ta soki Donald Trump

Kungiyar Al Shabab ta kasar Somaliya ta fito da wani sabon bidiyo na sukar mai neman takarar shugabancin kasar Amurka, a jam'iyyar Republican, Donald Trump.

Faifan bidiyon ya nuna irin kiran da Donald din ya yi kan a hana musulmi shiga kasar Amurka.

Kungiyar ta yi kira ga bakar fata 'yan Amurka da su karbi musulunci su kuma shiga a dama da su wajen yin Jihadi.

Ta ce akwai matsalolin wariyar-launin-fata da muzanta bakake da 'yan sanda su ke yi tare kuma da nuna kin jin musulmi a Amurka.

Har yanzu dai kungiyar kamfe ta Mista Trump ba ta mayar da martani ba.