Isra`ila: Za a Tsaurara Tsaro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Firayim Minsitan Isra`ila Benyamen Netanyahu

Firayim Ministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya ce za a tsurara tsaro a yankunan Larabawa da ke kasar, bayan harbe-harben da aka yi aTel Aviv, babban birnin kasar, a ranar Juma'ar da ta wuce.

Mista Netanyahu ya kunna wani kyandir a gaban wani gidan giya, inda wani dan bindiga ya bude-wuta, har ya kashe mutum biyu, yayin da mutum bakwai suka jikkata.

A halin da ake ciki dai Jami'an tsaro na ci gaba da farautar wanda ake zargi da kai harin, wanda inda suka ce dan shekara 29 ne da haihuwa mai suna Nashaat Melhem, kuma Balaraben Isra'ila ne daga kauyen Arara a arewacin kasar.

An dai nuna wani hoton bidiyo da ke nuna yadda dan bindigar ya zare wata bindiga mai sarrafa kanta daga wata jaka da yake goye da ita, kana ya bude-wuta a kan wani titi mai yawan gidajen barasa cike da jama'a.