Niger: An Rufe Karbar Sunayen `yan Takara

Image caption Tutar kasar Niger

A Jumhuriyar Nijar, an rufe karbar sunayen masu neman takarar shugaban kasa.

A jiya Asabar ne aka rufe karbar sunayen, da misalin karfe 12 na dare.

Duk da cewa a hukumance babu wanni bayani da ma'aikatar cikin gida ta yi kan sunayen 'yan takadar da suka mika takardunsu, rahotanni na cewa yanzu haka dai akalla mutum 16 ne aka gabatar da sunayensu karkashin jam'iyyun siyasa daban-daban, da kuma Indifanda, wadanda ba su tsaya karkashin wata jam'iyya ba.

Fitattu daga cikin wadanda rahotanni suka ambato, akwai shugaban kasar mai ci Alhaji Mahamadou Issoufou da Seyni Omar da Mahamane Ousmane da Cheiffou Amadou da Ibrahim Yacouba da Kassoum Moctar.

Sai ranar Alhamis 7 ga wannan watan Janairun ne za rufe karbar sunayen masu takarar kujerun majalisun dokokin kasar.

Yanzu dai kotun tsarin mulkin kasa ce za ta tantance 'yan takarar kafin su soma yakin neman zabe mako biyu gabanin ranar zabe, wato 21 ga watan biyu.