Amurka Ta Yi Tir Da Shugaba Kagame

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Rwanda Paul Kagame

Amurka ta yi amfani da wasu kausasan kalamai tana Allah-wadai da aniyar shugaba Paul Kagame ta yin ta-zarce a matsayin shugaban Rwanda.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Mista Paul Kagame ya bayyana aniyar tasa, bayan gagarumin goyon bayan da ya samu na yin gyaran-fuska ga kundin tsarin mulkin kasar don cire wani sashen da ya takaita wa shugaban kasa wa'adin mulki.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce shugaba Paul Kagame na wasa da damar da ya samu ta kafa tarihi wajen bunkasa demokuradiyya a Rwanda, abin da al'umar Rwanda suka dade suna kokarin rayawa tun bayan kisan kare-dangin da aka yi a kasar a shekarar 1994.