Vatican Da Palastine sun yi yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Paparoma Francis

Wata yarjejeniyar da fadar Fafaroma ta Vatican ta cimma da Hukumomin Palasdinawa bara, ta fara aiki gadan-gadan.

Yarjejeniyar dai ta kunshi damar da aka ba wa Cocin Katolika ya gudanar da harkokin ibada a wurare masu tsarki da ke karkashin ikon Palsdinawa.

Haka kuma yarjejeniyar ta jaddada goyon bayan fadar Vatican ga batun tabbatar da Palasdinu a matsayin kasa.

Isra'ila dai ta yi gargadin cewa yarjejeniyar za ta wargaza kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a yankin, tare da bata dangantakar da ke tsakaninta da fadar Vatican din.

Tun a shekara ta 2013 ne Fadar Fafaroma ta yi na'am da yunkurin Palasdinawa na neman 'yanci.