Al-Shabab: Trump ya mayar da martani

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Donlad Trump

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump ya tsaya kai da fata kan kiran da ya yi na a hana musulmai shiga Amurka.

Mista Trump wanda ya shaida wa gidan talbijin na CBS cewa yanzu ne ma mutane suke yaba masa kan maganar da ya yi.

Ya ce ba kowa ne mutum ba ne yake da karfin zuciyar da zai iya fadar wannan maganar ba duk kuwa da cewa al'amarin yana ci wa mutane da dama tuwo a kwarya.

Ya dai fadi haka ne martani ga wani faifan bidiyo da kungiyar masu ikrarin jihadi ta Al Shabab da ke kasar Somaliya ta fitar, a inda take kalubalantar dantakarar kan maganar da ya yi, a lokacin kamfe.

Kungiyar ta kuma nemi bakake 'yan Amurka da su shiga addinin musulunci sannan kuma su shiga a dama da su wajen Jihadi.