An yi girgizar kasa a Indiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Girgizar kasa a Indiya

An yi girgizar kasa a arewa-maso-gabashin India, kusa da iyakar kasar da Myanmar da Bangladesh.

Girgizar kasar dai ta kai 6.8 a ma'auni, kuma ta shafi yammacin birnin Imphal, babban birnin jihar Manipur.

Hucin girgizar kasar ya game yankin baki daya.

Tuni wasu mutane suka fara arcewa daga gidajensu.