Isra'ila: Bincike kan kisan Palasdinawa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

Masu gabatar da kara a Isra'ila sun tuhumi wasu Yahudawa biyu da laifin cinna wa gidan wasu Palasdinawa wuta da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku a yammacin kogin Jordan.

Binciken da 'yan sanda suke yi ya mayar da hankali ne a kan wata kungiyar wasu matasa masu kaifin kishin addini 'yan kabilar Yahudawa.

Ana tuhumar daya daga cikinsu da laifin kisan kai, yayin da shi kuma na biyun wanda matashi ne ake zargin yana da hannu a kisan kan.

Kisan Sa'ad da Riham Dawabsha da dansu Ali, mai watanni 18 da haihuwa, a wani kauye da ake kira Duma, a karshen watan Yuli, ya yi matukar tunzura Palasdinawa.