Za a bude Facebook na Kiristoci a Ghana

Hakkin mallakar hoto Loverealm
Image caption Za a gudanar da gwajin a cibiyar Pentecostal a Ghana

Wata kungiyar Kiristoci a Ghana ta ce za ta kaddamar da abinda ta kira tsarkakakkiyar hanya ta kafar sada zumunta musamman da za ta yi gogayya da shafin Facebook.

Kiristocin sun ce kafar ba za ta kunshi abubuwan da za su ci karo da Kiristanci ba.

Kungiyar da ake kira LoveRealm ta ce kafofin sada zumunta na zamani sun kunshi abubuwan batsa da tashe-tashen hankula.

Haka kuma ta kara da cewar kafar sada zumuntar da za ta kaddamar za ta bai wa masu son tuba kan sabon da suka yi dama, domin neman gafarar laifin da suka aikata.

Tuni kuma suka gayyaci dubban Kiristoci domin gwada shafin da suke son budewa.

Za a gudanar da gwajin ne a cibiyar Pentecostal dake Accra a Ghana.