Kasuwar hannun jarin China ta shiga cikin rudu

Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Hannayen jarin China sun yi munmunar faduwa

An dakatar da hada-hada a kasuwar sayar da hannayen jarin china bayan hannayen jarin sun yi mummunar faduwa.

Hannun jari nau'in Shanghai composite ya fadi da maki kusan 7 cikin 100, yayin da hannun jari nau'in blue chip CSI 300 ya fadi da kaso 7 cikin 100.

Kamfanin fasaha na Shenzhen shi ne wanda hannun jarinsa ya yi faduwa mafi muni da kaso sama da 8 cikin 100.

Tun farko dai an dakatar da hada hadar kasuwancin na minti 15 a kowacce rana bayan da hannun jarin ya fadi da kaso 5 cikin 100.

Hannayen jarin sun ci gaba da faduwa, lamarin da ya sa aka rufe hada-hadar kasuwar hannun jarin da wurin.