Shugabar IMF tana ganawa da Buhari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ms Largarde da ministar kudi, Kemi Adeosun da kuma gwamnan CBN Godwin Emefiele

Shugabar asusun bada lamuni na duniya, IMF, Christine Lagarde za ta ziyarci Nigeria domin ganawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Ana saran ganawar za ta kasance a ranar Talata a Abuja, domin tattauna hanyoyin farfado da tattalin arzikin Nigeria musamman yadda faduwar farashin mai yake tasiri ga kasar.

"Ina saran za mu yi tattaunawa mai ma'ana domin magance kalubalen tattalin arzikin kasar," in ji Lagarde.

Ms Lagarde kuma za ta gana da ministar kudin Nigeria, Kemi Adeosun a ziyarar ta kwanaki hudu a kasar.

Babu cikakkun bayanai kan tattaunawar, amma alama ce da ke nuna cewar asusun IMF, ya yi na'am da kamun ludayin gwamnatin shugaba Buhari.

A cikin watan Disamba ne, Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2016 da aka kiyasta shi a kan dala biliyan 31, wanda shi ne mafi yawa a tarihin kasar.