Iran na kokarin ganin an saki El-Zakzaky

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Shi'a na zanga-zanga domin a sako Zakzaky

Gwamnatin Iran ta ce tana bin dukkan hanyoyin difilomasiyya domin ganin hukumomin Najeriya sun saki shugaban kungiyar 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim al-Zakzaky .

Gwamnatin Najeriya ce ta kama shi a watan Disamba bayan takaddamar da ta faru tsakanin mabiyansa da sojojin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Hoseyn Jaberi-Ansari, ya shaida wa manema labarai a Tehran cewa, "Mun yi amfani da hanyoyi domin gargadin Najeriya a kan tsarewar da aka yi wa al-Zakzaky. Muna sa ran gwamnatin kasar za ta yi amfani da hikima domin ta sake shi."

A makon da ya gabata,Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai ce komai ba a kan batun har sai an kammala bincike.

Rikicin tsakanin 'yan Shi'a da sojojin Najeriya da ya auku a Zariya, ya janyo tayar da jijiyar wuya musamman a tsakanin masu kare hakkin bil adama a ciki da wajen Najeriya.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce an kashe sama da 'yan Shi'a 300 a rikicin na birnin Zariya.